in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta karfafa dangantaka da Namibiya a fannin makamashin hasken rana da iska
2016-08-30 10:19:59 cri

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin Zhang Dejiang ya bayyana a nan birnin Beijing jiya Litinin cewa, kasar Sin za ta karfafa dangantakarta tare da kasar Namibiya a bangaren makamashin hasken rana da na iska.

Kasar Sin za ta yi aiki tare da Namibiya domin yaukaka dadadar abokantakarta da yardar siyasa da juna domin kara bunkasa dangantaka a bangarorin makamashin hasken rana da iska, aikin kawar da gishiri daga cikin ruwan teku, tattalin arzikin teku, noma, kiwo da kamun kifi, in ji mista Zhang bayan ganawarsa tare da shugaban majalisar dokokin Namibiya, Peter Katjavivi.

Mista Zhang ya nuna cewa, musanya tsakanin hukumomin majalisun kasashen biyu na ci gaba da kasancewa wani muhimmin mataki na bunkasa huldar dangantaka, tare da yin kira ga majalisar wakilan kasar Sin APN da majalisar dokokin Namibiya da su ci gaba da karfafa dangantakarsu ta sada zumunta da huldarsu.

Mista Katjavivi ya bayyana godiya ga kasar Sin bisa ga namijin tallafi da taimakon cikin dogon lokaci da take kawowa kasar Namibiya, kuma ya nuna niyyarsa ta bunkasa huldar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Majalisar dokokin Namibiya tana fatan karfafa dangantakarta da kuma musanyarta tare da majalisar APN da kuma yin koyi da kasar Sin ta fuskar gudanar da mulki na gari, in ji mista Katjavivi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Shugaban NPC ya gana da shugaban kasar Togo 2016-05-31 21:03:04
v Zhang Dejiang ya gana da shugaba Buhari 2016-04-13 14:44:28
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China