A yayin ganawar tasu, Mr. Zhang Dejiang ya ce, Sin na fatan hada kai tare da Togo wajen tabbatar da daidaito game da batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda hakan zai baiwa kasar Togon damar cin gajiyar kudurorin da aka amince da su, a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Johannesburg a bara.
Shi kuma a nasa bangare shugaba Faure cewa ya yi, Togo tana fatan koyi daga saurin bunkasar da Sin ta samu, tare kuma da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, don tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron koli na Johannesburg.(Lubabatu)