in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masarautar Saudiyya ta amince da baiwa mata lasisin tuki
2017-09-27 10:55:32 cri
Sarkin masarautar Saudi Arabiya Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya fitar da dokar amincewa da baiwa mata izinin tuka mota a fadin kasar, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

Sabuwar dokar ta soke dokar hana mata tuki da ta shafe gwamman shekaru a kasar, a baya dai maza ne kadai aka sahhalewa tuka mota a cikin kasar ta Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarai na Saudi Press ya rawaito cewa, mafi yawan malaman addini a kasar Saudi suna ganin cewa, alfanun dake tattare da bai wa mata damar tuka mota ya fi hana su amfani.

Dokar hana mata tuka mota a kasar Saudi, ta tilastawa iyalai da dama daukar hayar direbobi wadanda za su dinga tuka iyalansu zuwa makarantu, wuraren aiki da sauran bukatu na yau da kullum.

Wata kididdiga ta baya bayan nan ta nuna cewa, kusan mazaje dubu 800 ne, mafi yawansu daga kudancin Asiya, suke gudanar da aikin tuka mota a kasar ta Saudiyya, kamar yadda gidan talabijin na Al Arabiya ya watsa.

Matan kasar Saudiya sun yi maraba da wannan sabuwar doka, inda suka bayyana ta a matsayin wata babbar nasara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China