Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar a jiya Jumma'a cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta riga ta amince da sayar wa kasar Saudiyya na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD da darajarsu ta kai kimanin dala biliyan 15.
Sanarwar ta ce, sayayyar kayayyakin soji da za a yi a wannan karo za ta habaka muradun Amurka a fannonin tsaron kasa da diplomasiyya, baya ga tallafawa Saudiyya wajen kara karfinta na kakkabo makamai masu linzami. Amma sayayyar ba za ta sauya daidaiton da aka samu ta fuskar soji a yankin Gabas ta Tsakiya ba.
Kasar Saudiyya kawa ce ga Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. Kuma Kasashen biyu sun taba daddale yarjejeniyar sayen makaman soji da darajarsu ta kai dala biliyan 110 a lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ziyarci Saudiyya a watan Mayun bana.(Kande Gao)