Rahotannin sun ce, wannan shi ne karon farko da 'yan tawayen Houthi suka kai harin makami mai linzami kan fadar mulkin kasar Saudiyya wato Riyadh, tun bayan da Saudiyya da wasu kasashe suka fara fatattakar 'yan tawayen shekaru biyu da suka shude.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudiyya ta fitar da wata sanarwa dake cewa, a halin yanzu filin jirgin saman birnin Riyadh na ci gaba da ayyukanta yadda ya kamata, babu wata matsala game da tashi ko saukar jiragen sama a filin jirgin.
Jiya Asabar da dare, an jiyo babbar karar fashewar wani abu a birnin Riyadh, mai tazarar kilomita 45 da filin jirgin saman birnin, yayin da dakarun kasar suka dakile harin daga kasar Yemen.
Tun a ranar 1 ga watan da muke ciki, dakarun hadin-gwiwar kasashe daban-daban dake karkashin jagorancin Saudiyya sun yi luguden wuta kan wani wuri dake arewacin kasar Yemen, inda 'yan tawayen Houthi suka ce, dakarun suka kai hari kan wani otel, lamarin da yayi sanadiyyar hallaka fararen-hula 26. Amma a cewar bangaren Saudiyya, dakarun sun kai hari ne kan wata matattarar 'yan tawayen Houthi, lamarin da ya yi ajalin mayakan da dama, ciki har da kwararru a fannin sarrafa makamai masu linzami.(Murtala Zhang)