in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Larabawa za su ci gaba da nuna adawa ga kudirin Amurka na maida Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'ila
2018-01-07 13:25:11 cri
Ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa guda shida, tare da babban sakataren gamayyar kasashen Larabawan sun yi wani taro a jiya Asabar a birnin Anman na kasar Jordan, inda suka jaddada rashin nuna amincewarsu da kuma yin adawa ga kudurin kasar Amurka na mayar da Kudus a matsayin fadar mulkin kasar Isra'ila. A cewarsu, kasashen Larabawa zasu ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayinsu kan batun na birnin Kudus.

Daga cikin mahalarta taron, akwai ministan harkokin wajen kasar Jordan, Ayman Safadi, da takwaransa na Palestine, Riyadal Malki, da ministan harkokin wajen kasar Saudiyya, Adel al-Jubeir, da takwaransa na kasar Masar, Sameh Shoukry, da ministan harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohammed Anwar Gargash, da ministan kula da harkokin waje da hadin-gwiwar kasa da kasa na kasar Morocco, Nasser Bourita, tare kuma da babban sakatare na gamayyar kasashen Larabawa wato Ahmad Abdoul Gheit.

A gun taron manema labarai da aka yi, Gheit ya ce, kasashen Larabawa sun zama tsintsiya madaurinki daya kan nuna adawa da kudurin Amurka, na maida Kudus a matsayin fadar mulkin kasar Isra'ila. Ya kuma ce, kasashe mahalarta taron za su ci gaba da nacewa ga bin matsayinsu kan wannan batu.

Shi kuma a nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Jordan, Ayman Safadi cewa ya yi, kasashen Larabawan na fatan kara samun kasashen da zasu amince Palestine a matsayin wata kasa. Ya ce, idan ba'a iya kafa wata 'yantacciyar kasar Palestine mai hedkwata a gabashin Kudus ba, ba za'a iya kai ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya ba.

A ranar 6 ga watan Disambar bara, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da amincewa ga Kudus a matsayin fadar mulkin kasar Isra'ila, kana Amurka zata fara aikin kaurar da ofishin jakadancinta daga birnin Tel Aviv zuwa Kudus, lamarin da ya samu adawa daga kasashen duniya da dama.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China