Cikin jawabin da ya gabatar ta gidan radiyon Palastinu, Erekat yace, kuri'ar da majalisar Israeli Knesset ta kada, da kuma matakin da jami'yyar Likud ta dauka na kwace ikon yamma da kogin Jordan sakamako ne na matakin da Trump ya dauka na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila a ranar 6 ga watan Disambar shekarar bara.
Erekat ya fada cewa, wannan yana daya daga cikin sabuwar dangantakar hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila na yin mulkin kama-karya da kuma lalata manufofin wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, ya kara da cewa, shugaban Palastinawa Mahmoud Abbas, ya ayyana wasu dabarun da Palastinawa zasu yi amfani dasu wajen tunkarar wannan al'amari don magance matsalar Palastinawan.(Ahmad)