Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Palestinu na cewa, shugaba Mahmoud Abbas na ganin cewa, Amurka na goyon bayan Isra'ila kan matsayin birnin Kudus, kuma, daftarin da Amurka ta gabatar, sun saba da dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin MDD.
A cewar Shugaban, jama'ar Falesdinu ba sa son Amurka ta shiga aikin neman sulhun, kuma ba za su amince da daftarin da Amurka ta gabatar da su kan lamarin ba.
Bugu da kari, shugaba Abbas ya ce, amincewa da Amurka ta yi da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, ya sabawa dokokin kasa da kasa, yana mai jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da dukufa wajen neman 'yanci da mulkin kai. (Maryam)