in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falesdinu ta yabawa MDD kan kudurinta game da matsayin birnin Kudus
2017-12-22 15:36:17 cri
Jiya Alhamis, fadar shugaban Falastinawa ta fidda wata sanarwa, inda ta yabawa MDD kan kudurinta game da matsayin birnin Kudus.

Cikin sanarwar, kakakin fadar shugaban falastinawan Nabil Abu Rudeineh, ya bayyana cewa, kudurin da aka zartas a zauren MDD ya nuna goyon bayan da gamayyar kasa da kasa suka nunawa al'ummar Falastinawa wajen kare ikonsu, kana ya kuma nuna goyon bayan da dokar kasa da kasa ta yiwa Falesdinu.

Haka kuma ya kara da cewa, bisa dokar kasa da kasa, birnin Kudus ya kasance yanki ne da aka mamaye, kuma ba wanda zai iya yin tababa kan wannan batu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China