in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban zauren MDD ya amince da wani kuduri game da matsayin birnin Kudus
2017-12-22 10:24:33 cri
Babban zauren MDD ya amince da wani kuduri game da matsayin birnin Kudus, wanda zai hana tasirin matakin Shugaban Amurka Donald Trump na daukar birnin a matsayin babban birnin Isra'ila.

A wani zama na gaggawa da ba a saba yi ba, kudurin da kasashen Turkiyya da Yemen suka gabatar, ya samu kuri'un amincewa daga kasashe 128, yayin da 9 suka ki, inda 35 kuma suka kauracewa kada kuri'ar.

Kasashe 9 da suka ki amincewa da kudurin sun hada da Amurka da Isra'ila da Togo da dai sauransu.

Kudurin ya tabbatar da cewa, duk wani mataki ko yunkuri da zai sauya matsayin birnin Kudus mai tsarki ba shi da wani tasirin doka, kuma dole ne a yi watsi da shi bisa kudurorin kwamitin sulhu na majalisar. A saboda haka, ya yi kira ga dukkan kasashe su kauracewa kafa wani shirin diflomasiyya a birnin na Kudus.

Ya kuma bukaci mambobin MDD su yi biyayya ga kudurorin kwamitin sulhu game da birnin Kudus, kana su yi watsi da duk wani mataki da ya sabawa hakan.

Irin wannan kuri'ar ta MDD ba ta zama doka, sai dai, amincewar ya nuna kuduri na bai daya da kasashen ke da shi, sannan abu ne mai karfi ta fuskar siyasar duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China