Shugaban na Sin wanda kuma shi ne babban sakatare na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis mai mulki a kasar(JKS), kuma shugaban kwamitin tsakiya na hukumar rundunar sojin kasar ta Sin, na cikin manyan jagororin kasar da suka halarci taron na yini 3.
Taron na shekara shekara, wanda ya maida hankali wajen tsara alkiblar da kasar za ta sanya gaba ta fannin tattalin arziki a shekarar 2018 mai kamawa, ya kuma shaida tunanin shugaban na Sin a matsayin "wani jari mai daraja" ga JKS dama kasar ta Sin baki daya.
Sanarwar ta ce ya zama wajibi a ci gaba da bin tafarkin wannan tunani, tare da nacewa aiwatar da shi domin wanzar da ci gaban kasar ta Sin.