Sanarwar ta ce za a kara maida hankali ga fannin inganta tattalin arzikin kasar, a maimakon maida hankali ga saurin bunkasa kadai ba. Hakan dai na nufin za a fadada samar da kayayyaki masu nagarta kirkirar kasar Sin, a madadin kirar kasar kawai.
A daya hannun kuma, kasar ta Sin a cewar sanarwar za ta kara kaimi, wajen yaki da talauci cikin shekaru 3 masu zuwa. Har ila yau za a maida hankali wajen dakile gurbatar muhalli tsakanin wadannan shekaru.
Wani batun na daban kuma da sanarwar ta kunsa, shi ne na ingnata tsarin shigo da kayayyaki daga ketare, domin samar da daidaito na cinikayya da sauran kasashen ketare.
Sanarwar ta ce za a rage harajin shigo da wasu nau'o'in kayayyaki, domin baiwa kasuwa damar daidaita da kuma rage gibin cinikayya.
An dai gudanar da taron yini 3 na masu ruwa da tsaki game da tattalin arzikin kasar Sin a matakin koli ne a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, taron da jagororin kasar suka yi amfani da shi, wajen nazartar yanayin tasirin tattalin arzikin kasar a shekarar nan ta 2017, tare da fidda tsare tsaren da za a sanya gaba a shekara mai kamawa.