Oshoala mai shekaru 23, ta doke sauran 'yan takara na Afirka ta Kudu da kuma na kasar Kamaru. Game da hakan, Oshoala ta bayyana cewa, a shekarar 2017 ta sauya sheka daga kungiyar Arsenal ta kasar Ingila zuwa kungiyar Quanjian ta birnin Dalian dake nan kasar Sin, kuma mutane da dama sun nuna shakku game da wannan mataki na ta, amma ta yi imani da kanta, don haka ta samu lambar yabo a wannan karo.
An haifi Oshoala a ranar 9 ga watan Oktoba na shekarar 1994 a Ikorodu dake tarayyar Nijeriya, ta kuma taba buga wasa a kungiyar Liverpool da ta Arsenal ta kasar Ingila. A gasar wasan kwallon kafa ta matasa ta duniya da aka gudanar a shekarar 2014, ta samu lambar yabo ta 'yar wasan kwallon kafa mafi kwarewa, da kuma ta 'yar wasan kwallon kafa da ta fi zura kwallaye a raga, kana ta zama 'yar wasan kwallon kafa matasa mata mafi kwazo, da kuma 'yar wasan kwallon kafa mata mafi kwarewa ta nahiyar Afirka a wannan shekara.
Har wa yau ita ce 'yar wasa mafi shahara a kungiyar wasan kwallon kafar mata ta Nijeriya.
A shekarar 2016, ta jagoranci kungiyar wasan kwallon kafa mata ta Nijeriya inda suka cimma nasara a gasar wasan kwallon kafa ta kasashen Afirka, don haka ta samu lambar yabo ta 'yar wasan kwallon kafa mata mafi kwarewa ta nahiyar Afirka ta shekarar 2016.
A watan Febrairu na shekarar 2017, Oshoala ta fara taka leda a kungiyar Quanjian dake birnin Dalian na kasar Sin, inda ta taimakawa kungiyar wajen kare kambi a gasar wasan kwallon kafar mata ta Super League ta kasar Sin ta shekarar 2017, kana ta zama 'yar wasan kwallon kafar mata mafi zura kwallaye a raga a wannan karo. (Zainab)