in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da dan wasan kasar Uganda Denis a matsayin gwarzon dan wasan Afrika na shekarar 2016
2017-01-07 13:01:50 cri
A ranar Alhamis ne aka ba mai tsaron ragar kasar Uganda Denis Onyango lambar yabo ta gwarzon dan wasan Afrika na shekarar 2016.

Onyango wanda ya taimaka wa Uganda a wasan samun cancantar shiga gasar cin kofin Afrika ta bana, bayan ya shafe shekaru 39 yana dako, ya karbi wannan lambar yabo ne yayin bikin ba da lambar yabo na GLO Confederation African Football da ya gudana a Abuja, babban birnin Najeriya.

Onyango ya samu kuri'u dari biyu da hamsin da biyu, inda dan kungiyarsa ta Sundowns kuma dan wasan tsakiyar Zimbabwe Khama Billiat ya samu kuri'u dari biyu da ashirin da takwas, yayin da Rainford na kasar Zambia ya zo na uku da kuri'u dari biyu da shida.

Onyango na kuma cikin jerin masu tsaron raga 'yan Afrika goma sha daya da suka yi fice.

An kuma zabi kungiyar kwallon kafar Uganda ta Cranes a matsayin kungiyar da ta yi wa sauran kungiyoyi fintinkau, saboda rawar da ta taka da ya kai ta ga samun cancantar shiga gasar cin kofin Afrika ta bana.

Kungiyar Cranes ta doke kungiyoyin kasashen Zimbabwe da Senegal da suka yi takara tare. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China