in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afirka za su goyi bayan Hayatou a matsayin shugaban CAF
2017-03-08 11:20:59 cri

Babban sakataren kungiyar gamayyar hukumomin kwallon kafar kasashen gabashi da tsakiyar Afirka ko CECAFA a takaice Nicholas Musonye, ya ce za su goyi bayan shugaban hukumar kwallon kafar Afirka CAF na yanzu Issa Hayatou, ya zarce kan karagar jagorancin hukumar, yayin sabon zaben dake tafe nan gaba cikin wannan wata na Maris.

Nicholas Musonye, ya bayyana hakan ne a birnin Nairobi, yana mai cewa, suna fatan Hayatou 'dan asalin kasar Kamaru, wanda kuma ke rike da ragamar hukumar CAF tun cikin shekara 1988, zai samu damar kara darewa karagar jagorancin kungiyar a zangon shekaru 4 masu zuwa. Mr. Musonye dai ya danganta goyon bayan na su ga Hayatou, da irin kwazon sa wajen ciyar da harkokin kwallon kafar yankin gaba.

Yanzu dai haka Hayatou wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, zai fafata da abokin takarar sa Ahmad Ahmad daga kasar Mauritius. Ahmad Ahmad dai shi ne shugaban hukumar kwallon kafar kasar sa FA, kuma yana samun goyon bayan shugaban FIFA Gianni Infantino.

Nan gaba cikin watan nan na Maris ne za a gudanar da zaben sabon shugaban hukumar CAF a birnin Addis Ababan kasar Habasha.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China