in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru ta doke Morocco a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka ta 2019
2017-06-11 13:05:28 cri
A wasan farko na rukunin B na neman shiga gasar cin kofin Afirka na shekarar 2019 da aka gudanar a ranar 10 ga wata, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Kamaru ta doke ta kasar Morocco da ci daya da nema. Wannan ne karo na farko da mai daukar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta 2019 kasar Kamaru ta yi wasa a wannan karo.

Kungiyar wasan Kamaru da ta Morocco, sun yi wasan ne a filin wasa na Ahmadou Ahidjo dake birnin Yaoundé na kasar Kamaru. A yayin wasan, Vincent Aboubakar, dan wasan kungiyar Kamaru ya ci kwallo daya a mintoci 30 da fara wasan. A zagayen karshe a wasan, kungiyar Morocco ta yi ta kokarin kai hare-hare kan gidan kungiyar Kamaru, amma ta gaza zara kwallon.

Kocin kungiyar kasar Morocco ya bayyana a gun taron manema labaru bayan wasan cewa, kungiyar Kamaru tana da karfi, amma kungiyarsa ta Morocco ba ta yi wasa mai kyau a zagayen farko na wasan ba, kuma ta yi ta barar da kwallaye masu yawa. Kana kocin kungiyar Kamaru ya nuna gamsuwa ga kungiyarsa game da wannan wasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China