Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Morocco ta sanar da cewa, kasar ce za ta karbi bakuncin gasar zakarun nahiyar Afrika ta badi.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an yanke shawarar ba Morocco damar daukar bakuncin wasan ne yayin wani taron da kwamitin hukumar kwallon kafar Afrika ya yi ranar Asabar da ta gabata a Lagos dake Nijeriya.
Sanarwar ta ce, an zabi Morocco ne saboda yanayin ci gaba da take da shi a fannonin kayayyakin more rayuwa da filayen wasanni da kayayyakin ba da horo da otel-otel da asibitoci da kuma hanyoyin sufuri.
Biranen 4 da suka hada da cibiyar harkokin tattalin arzikin kasar wato Casablanca, da Tangier dake arewacin kasar, da kuma Marakesh da Agadir dake yankin kudanci ne za su karbi bakuncin gasar.
A baya, an tsara cewa kasar Kenya ce za ta karbi bakuncin gasar, sai dai an karbe daga hannunta saboda rashin kyawun shirye-shirye.
An tsara gudanar da gasar wadda za a yi tsakanin 'yan wasan nahiyar Afrika daga ranar 12 ga wata Junairu zuwa 4 ga watan Fabrerun 2018. (Fa'iza Mustapha)