Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya jinjinawa kwazon da tawagar kwallon kafar kasarsa ta nuna, na lashe kofin gasar kwallon kafar nahiyar Afirka na bana wadda ta gudana a kasar Gabon.
Kamaru ta doke Masar a wasan karshe da suka buga ranar Lahadin karshen mako da ci 2 da 1, inda ta dauki kofin wannan gasa a karo na 5. Kafin hakan Kamaru ta dauki wannan kofi na nahiyar Afirka a shekarar 1984 a kasar kwadebuwa, da 1988 a Morocco, da shekarar 2000 a Najeriya, da kuma shekara ta 2002 a kasar Mali.
Kafin fara gasar dai ba a zata Kamaru za ta taka wata rawar gani ba, kasancewar a gasar shekarar 2015 wadda ta gudana a Equatorial Guinea, an cire ta tun a wasannin rukuni.
Da yake yabawa tawagar 'yan wasan da jami'an su, yayin wata liyafa da aka shirya a fadar gwamnatin kasar a jiya Laraba, shugaba Biya ya ce, kasarsa ta farfado a fannin kwallon kafa. Ya ce, shi da al'ummar kasarsa na matukar alfahari da nasarar kungiyar.
A watan Disambar bara ma dai shugaba Biya ya furta makamantan wadannan kalamai, lokacin da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar ta zo na biyu a gasar nahiyar ajin mata karo na 10.(Saminu)