in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta yabawa sakin 'yan matan Chibok sama da 80
2017-05-08 11:17:56 cri
Asusun hukumar tallafawa kananan yara ta MDD (UNICEF) ta yi murna da sako 'yan matan sakandaren Chibok sama da 80 a ranar Asabar din da ta gabata wadanda mayakan Boko Haram ke rike da su shekaru 3 da suka gabata a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Sanarwar da UNICEF ta fitar, ta bayyana cewa wannan lamarin abun farin ciki ne kasancewar ranar da wadannan 'yan matan za su sake ganawa da iyalansu ta zo.

Hukumar ta MDD ta bayyana cewa za ta tallafawa gwamnatin Najeriya wajen samar da abubuwan da ake bukata wajen kulawa da tunanin yaran da aka ceto.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar za ta taimaka wajen jagorantar yaran domin sake sada su da iyalansu da kuma tabbatar da cewar sun cigaba da karatunsu a waje mai cike da tsaro.

Da ma dai tuni jami'an na UNICEF suka mika wasu kayayyakin kula da lafiya, kuma suka gudanar da binciken lafiyar 'yan matan gabbanin a taho dasu.

Cikin sanarwar, UNICEF ta bukaci Boko Haram data kawo karshen cin zarafin kananna yara, musamman yin garkuwa da yara da yin lalata da su da kuma tilastawa yara mata yin auren dole.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China