Mataimakin shugaban kwamitin shugaban kasar, kan farfado da yankin arewa maso gabas, Tijjani Tumsah, ya ce an dauki dukkan matakan da suka dace na tabbatar da ba a sake samun aukuwar makamancin abun da ya faru na sace 'yan mata a shekarar 2014 ba.
Tijjani Tumsah, ya ce za a samar da da wani tsari na samar da bayanai da yin gargadi kan lokaci domin tsaron 'yan matan.
Ya ce kwamitin na duba yuwar samar da wasu shirye-shirye da za su taimaka wajen saita tunanin matasan, ta yadda zai dace da manufofin gwamnati mai ci a kasar.( Fa'iza Mustapha)