in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Nan gaba kadan wasu Karin 'yan matan na Chibok za'a ceto su
2017-05-08 10:19:03 cri
Ministan sadarwa na Najeriya, Adebayo Shittu, ya bayyana cewa yana da kyakkyawar fata nan gaba kadan za'a sake ceto karin 'yan matan sakandaren na Chibok daga hannun mayakan Boko Haram.

A ranar Asabar din da ta gabata ne, aka sako 'yan matan 82, bayan cimma yarjejeniya, inda aka yi musayar 'yan matan ta hanyar sakin wasu daga cikin mayakan Boko Haram da gwamnati ke tsare da su.

Da yake jawabi a wani taro a Ibadan, kudu maso yammacin kasar, ministan ya ce nan gaba kadan za'a sake sako wasu karin 'yan matan dake hannun mayakan ta hanyar cimma matsaya tsakanin gwamnatin Najeriyar da mayakan.

A wani labarin kuma kungiya mai fafutukar ganin an sako 'yan matan na Chibok wato Bring Back Our Girls Group (BBOG), ta yaba wa gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaron kasar saboda samun nasarar ceto 'yan matan 82.

Sanarwar yabon na dauke da sa hannun shugabar kungiyar fafutukar kuma tsohuwar minista, Oby Ezekwesili, wanda aka fitar a jiya Lahadi a Abuja, babban birnin kasar.

Tace an yi nasarar ceto 'yan matan ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da sojoji, da gwamnatin Switzerland, da kungiyar Red Cross, da kuma sauran kungiyoyi na cikin gida da na kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China