Rahotanni daga jihar dai sun tabbatar da cewa, wani saurayi ne dauke da damarar ababen fashewa ya kutsa kai cikin masallacin dake garin na Gamboru, yayin sallar Asubar Larabar nan, ya kuma tada ababen fashewar dake jikin sa.
An ce cikin mutane 10 da suka rasu hadda mahaifin dan kunar bakin wajen. Tuni kuma aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Wani mazaunin yankin da ya shaida aukuwar lamarin mai suna Abba Lawan, ya ce kafin aukuwar hakan, matashin dan kunar bakin waken ya kauracewa danginsa, ya koma daji inda 'yan ta'adda suke samun mafaka. (Saminu Hassan)