in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta inganta tsaron tekun kasar
2017-12-31 15:20:20 cri
Wani kusa a hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwan Najeriya NIMASA, ya ce, gwamnati za ta tsara wasu muhimman dabaru da nufin tabbatar da tsaron teku, da bada kariya ga hajoji da manyan jiragen dakon kaya a tekunan kasar.

Darakta janar na hukumar ta NIMASA Dakuku Peterside ya fadawa 'yan jaridu a Lagas cewa, wannan na daga cikin muhimman tanade-tanaden da gwamnatin kasar ke yi na tabbatar da tsaron tekunan kasar, ya ce a kwanan nan ne majalisar zartaswar kasar a Abuja, babban birnin kasar ta rattaba hannu don amincewa da wannan tsari.

Peterside ya sanar da kafa cibiyar gudanar da harkokin tekun a matsayin wani bangare na dabarun tabbatar da tsaron tekunan kasar.

Ya ce an tanadi wasu tsare-tsare 4 da suka hada da shirin wayar da kai a game da yanayin da ake ciki, da samar da damar kai dauki, da aiwatar da dokoki, da kuma yin hadin gwiwa da sauran sassa na cikin gida da na shiyyoyi, wadannan sun kasance a matsayin wasu ginshikai da aka tanada don magance matsaloli masu aikata laifukan fashin teku.

A cewarsa, aiwatar da dabarun tsaron tekun na NIMASA, ta hanyar yin hadin gwiwa da abokan huldarta, su ne manyan matakan da za'a bi wajen dakile masu fashin teku da sauran masu aikata muggan laifuka a gabar manyan tekunan kasar.

Ya nanata cewa, hukumar ta NIMASA za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da sojojin Najeriyar, musamman sojojin ruwa da na sama, domin tabbatar da tsaron tekunan kasar baki daya.

Darakta janar din ya bayyana cewa, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, a kokarin da take na tabbatar da ganin an amince da dokar da ta shafi yaki da fashin teku, wanda tuni majalisar zartaswar kasar ta gabatarwa majalisar dokokin kasar domin neman amincewarta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China