Wata sanarwa da ta shiga hannun Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta ruwaito shugaba Buhari na bayyana al'amarin a matsayin wanda bai dace ba, da ba za a taba amincewa da shi ba.
Da safiyar ranar Litinin ne wasu 'yan bindiga suka farwa gida basaraken yankin Sanga na jihar Kaduna dake arewa maso tsakiyar kasar, inda suka kashe shi tare da matarsa. Haka zakila a ranar ne aka kai harin kan wasu mutane dake dawowa daga coci bayan gudanar da addu'ar shiga sabuwar shekara a jihar Rivers mai arzikin man fetur. Sannan kuma a jiya Talata a aka kai wasu hare-hare a yakunan Guma da Logo na jihar Benue. Hare-haren da suka yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama.
Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro dake jihohin su kara matse kaimi a kokarin da suke don gaggauta tabbatar da maharan sun fuskanci fushin hukuma.
Shugaban ya kuma yi kira ga al'ummar yankunan da su guji daukar fansa, inda ya bukaci su ba hukumomin tsaro damar gudanar da bincike don tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu. (Fa'iza Mustapha)