in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 21 sun mutu sanadiyyar harbin kan mai uwa dawabi da aka yi kan wasu da suka fito daga mujami'a a Najeriya
2018-01-03 10:22:55 cri

A kalla mutane 21 ne ake fargabar sun mutu sanadiyyar bude musu wuta da wasu 'yan bindiga da suka yi da daren ranar Litinin a jihar Rivers mai arzikin man fetur .

A cewar shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ruwa da tsaron gabar teku Dakuku Peterside, ana zargin 'yan bindigar da bude wuta kan tawagar wasu mutane dake kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun fito daga addu'ar shiga sabuwar shekara a yankin Ogba-Egbema-Ndoni na jihar.

Dakuku Peterside wanda ya fito daga yankin, ya ce ana zargin 'yan bindigar 'yan kungiyar asiri ne dake fafautukar neman karfin iko.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, 'yan bindigar sun yi harbin kan mai uwa dawabi ne a kan mutanen.

Rundunar 'yan sandan jihar da ta tabbatar da harin, ta ce ana gudanar da bincike don zakulo wadanda ke da hannu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China