in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin da aka kaddamar a bikin sabuwar shekara ya kashe mutune biyu a arewacin Najeriya
2018-01-02 09:54:57 cri
Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kaddamar da hari kan kauyen Arak dake yankin arewacin jahar Kaduna a lokacin bikin sabuwar shekara, inda suka hallaka wani babban basaraken Etum Numana ll, Gambo Makama tare da matarsa mai dauke da juna biyu.

Mai magana da yawun 'yan sandan jahar Mukhtar Hussaini Aliyu, ya tabbatarwa 'yan jaridu faruwar lamarin, sannan daya daga cikin 'yayan basaraken ya samu raunuka, kuma an kone gidansa kurmus a lokacin harin.

Wannan shi ne hari na uku na baya bayan nan da aka kaddamar a kudancin Kaduna cikin mako guda.

Basaraken wanda sarkin gargagajiya ne mai daraja ta 2, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya tashi daga fadarsa dake Gwantu inda ya nufi kauyensu na Arak, da nufin halartar bikin sabuwar shekara tare da talakawansa, inda aka hallaka shi.

Kakakin 'yan sandan ya bukaci a kwantar da hankulla kasancewa jami'an hukumar na iya bakin kokarinsu domin gudanar da bincike kan lamarin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China