in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 50 sun mutu sanadiyyar wani hari da makiyaya suka kai a Nijeriya
2018-01-03 10:11:16 cri

A kalla mutane 50 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, sanadiyyar wani hari da Fulani makiyaya suka kai kan al'ummar kabilar Tivi a jihar Benue dake arewa maso tsakiyar kasar.

Da yake zantawa da manema labarai a Makurdi babban birnin Jihar, Gwamna Samuel Ortom ya ce an yi wa mutane yankan rago, yayin da aka kashe yara, sannan aka guntule hannayen wassu da dama yayin harin da aka kai jiya Talata.

Samuel Ortom ya ce an kuma kashe masu tsaron abbobin gida 9, yayin da aka kona motarsu ta sintiri kirar Hilux.

Har ila yau, Gwamnan ya dora laifin gazawa wajen kare al'umma a kan Gwamnatin Tarayyar kasar.

Ya ce an sanar da Gwamnatin Tarayyar game da barazanar makiyayan, wadanda suka lashi takobin adawa da dokar hana kiwo da Gwamnatin jihar ta sanya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China