Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin tana fatan ganin ci gaban kasashe a fannin bincike da kuma yadda suke amfani da sararin samaniya domin samun ci gaba.
A game da kalaman da Trump ya yi cewa, akwai hanyoyi da dama game da amfani da sararin samaniya, ciki har da harkokin da suka shafi soja. Lu Kang ya ce, har kullum kasar Sin tana adawa da duk wani mataki na amfani da sararin samaniya domin yada makamai. Haka kuma kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su cimma daidaito game da hana yaduwar makamai a sararin samaniya.
A jiya ne shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya hannu kan wata doka a karon farko a hukumance, inda ya umarci hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA da ta sake tura 'yan sama jannati zuwa duniyar wata daga bisani kuma su wuce duniyar Mars. (Ibrahim Yaya)