in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An canza sojojin injiniyoyin kasar Sin da suke aikin kiyaye zaman lafiya a Sudan
2017-12-28 19:59:24 cri
A yau Alhamis ne sojoji injiniyoyi na kasar Sin guda 116, wadanda ke cikin kungiya ta 2 ta rukuni na 14 na sojoji injiniyoyi dake aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, suka isa sansanonin Nyala da na Ed Daein, inda suka maye gurbin sojojin da za su kammala wa'adin ayyukansu.

A yayin taron mika aiki da sojojin suka kira, hafsa mai kula da rukunin sojojin, Bi Xianbo, ya ce za su gaji al'ada mai kyau ta sojojin injiniyoyi na kasar Sin, tare da gudanar da aiki yadda ya kamata, don daukaka matsayin kasar Sin a idon duniya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China