Shugaban wanda ya bayyana haka a jiya Lahadi, yayin bikin zagayowar shekaru 62 da samun 'yancin kan kasar, ya ce wannan aiki zai shafi duk wasu sassa na tabbatar da tsaro, da kandagarkin aukuwar laifuka, tare da tabbatar da an dakile masu fatan tarwatsa 'yancin kan kasar ko albarkatunta.
Shugaba Al-Bashir ya kara da cewa, duk wani yunkuri na samar da sulhu da hadin kan kasa ba zai yi tasiri ba, muddin aka gaza samar da managarcin tsaro.
Daga nan sai ya jaddada aniyarsa ta aiki tare da sauran kasashen duniya a fannin hadin gwiwa, domin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da tsaron yankuna, da kuma sassan kasa da kasa. Baya ga yunkurin dakile ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda da masu safarar kudade ko bil Adama. (Saminu Hassan)