in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan gudun hijirar Sudan 1,500 sun amince su koma gida
2017-12-13 11:13:07 cri
Babbar hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR a takaice, ta ce kusan 'yan gudun hijira 1,500 na kasar Sudan, sun amince su koma kauyen Dafaq dake jihar kudancin Darfur.

Wata sanarwa daga hukumar ta UNHCR, ta ce a ranar Talata kaso na farko na wadannan 'yan gudun hijira mai kunshe da mutane 45 ya isa filin jirgin saman Nyala. Ana kuma sa san cewa mutanen za su yada zango na kwanaki 3 a fadar mulkin jihar kudancin Darfur, kafin karasawa kauyen nasu wanda ke da nisan kilomita 350 daga Nyala.

Sanarwar ta rawaito wakiliyar hukumar ta UNHCR a kasar Sudan Noriko Yoshida, ana maraba da wadannan 'yan gudun hijira da komawa gida. Jami'ar ta kuma jaddada kudurin hukumar ta da ma hukumar COR mai tallafawa 'yan gudun hijira, na ci gaba da bibiyar halin da wadanda suka koma yankunan na su ke ciki.

A yanzu haka dai kusan 'yan gudun hijirar Sudan 592,000 ne suka tsallaka kasar Chadi, kana wasu 392,000 ke samun mafaka a sansanonin gabashin kasar 13, yayin da kuma ragowar 200,000 ke zauna a yankunan kan iyakar kasashen, da kuma wasu biranen kasar ta Chadi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China