Shirin rawar dajin ya samu halartar rundunonin soji daga kasashen Sudan, Somalia, Djibouti, Kenya, Uganda, Seychelles, Comoro Islands, Habasha, Rwanda da Burundi.
Ministan tsaron kasar Sudan Awad ibn Auf, wanda ya jagoranci bikin kammala taron ya bayyana cewa, dakarun na EASF a shirye suke su tunkari mayakan 'yan ta'adda dake zaune tsaye a wasu kasashen dake shiyyar.
Shugaban shirin EASF, Ambassador Issimail Chanfi, wanda ya gabatar da jawabi a lokacin bikin ya ce, shirin rawar dajin ya tabbatar da daga matsayin EASF na kasancewa kwararru, kuma a halin yanzu EASF tana da karfin da za ta iya tunkarar shirin wanzar da zaman lafiya a zahiri.
A shekarar 2004 ne aka kafa dakarun ko-ta-kwana na EASF a matsayin da ya daga cikin tawagogin dakarun wanzar da zaman lafiya biyar da ake da su a Afrika, kana an dora mata alhakin wanzar da zaman lafiya da tsaro a shiyyar gabashin Afrika. (Ahmad Fagam)