in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta musanta yiwuwar karin kudin man fetur
2017-12-27 09:04:34 cri
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta batun da wasu kafafen watsa labaran kasar ke yadawa, cewa tana shirin kara farashin man fetur a shekarar 2018 dake tafe.

Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a jihar Lagos, yana mai cewa karancin mai da ake fama da shi a fadin kasar ya faru ne sakamakon karancin sa a rumbunan ajiya dake sassan kasar daban daban.

Mr. Osinbajo ya kuma bayyana kudurin gwamnatin kasar na hukunta dukkanin wani mai gidan mai da aka samu da laifin boye man domin cin kazamar riba. Ya ce gwamnatin Najeriyar na yin duk mai yiwuwa, wajen ganin ta kawo karshen matsalar man da 'yan kasar ke fuskanta yanzu haka.

Mataimakin shugaban kasar dai ya kai ziyarar ba zata wasu gidajen mai dake jihar Lagos a jajiberin ranar bikin kirismeti, inda ya leka yankin Lekki da kewaye, domin ganewa idanunsa halin da ake ciki game da karancin mai a jihar.

A ranar Lahadin karshen mako ne dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya baiwa al'ummar Najeriya hakuri bisa halin matsi da suka shiga, sakamakon karancin mai da ya karade sassan kasar. Shugaba Buhari ya ce tuni ya baiwa hukumomin dake lura da sashen umarnin kara matsa kaimi, domin tabbatar da sun dakile yunkurin wasu daga dillalan mai dake kara mafashin sa ga al'umma. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China