in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fama da karancin man fetur a dai dai lokacin bukukuwan kirsimeti a Najeriya
2017-12-24 13:41:27 cri
Yayin da ake jajiberen shagulgulan kirsimeti da na sabuwar shekara, 'yan Najeriya da dama na fuskantar matsalar karancin man fetur a fadin kasar.

Duk da yunkurin shiga yajin aikin da kungiyoyin ma'aikatan man fetur na kasar suka yi, wanda ya yi sanadiyyar wasu suka dinga saya suna boye man kafin daga bisani aka janye yunkurin, lamarin ya haifar da matsalar wahalar man da kuma dogayen layuka a gidajen man a mafi yawan yankunan kasar, lamarin da ya baiwa 'yan bunburutu damar cin karensu babu babbaka.

Masu ababen hawa da dama sun koka dangane da karancin man a mafi yawan gidajen sayar da man fetur din a birnin Legas, suna masu bayyan cewa, lamarin zai iya shafar masu son yin tafiye tafiye don halartar bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.

A halin yanzu, ana sayar da litar man ne a kan naira 250 a mafi yawan gidajen man dake sayar da man a kasar.

Maikanti Baru, shi ne shugaban kamfanin man fetur na kasar (NNPC), ya zargi manyan dillalan mai da laifin haddasa karancin man a kasar.

Sannan ya bayyana cewa, jita jitar da ake bazawa na yiwuwar kara farashin man ya kasance daya daga cikin dalilan da suka haddasa matsalar, inda yace wasu daga cikin dillalan man sun yi ta saya suna boye man da nufin sayar da shi a farashi mai tsada.

Baru ya bada tabbacin cewa kamfanin man ya ninka adadin man da yake samarwa, daga manyan motocin dakon man kimanin 700 dake daukar lita miliyan 27-30, inda ya koma litar man miliyan 80 tun daga lokacin da aka fara fuskantar matsalar karancin man a kasar.

Sannan ya baiwa al'ummar Najeriya tabbacin cewa, hukumar ta NNPC tana da isasshen mai wanda zai kai har tsawon kwanaki 30, kuma a wannan makon matsalar karancin man za ta zo karshe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China