Lu Kang wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai a birnin Beijing, ya ce kasar Sin tana taya wa kasar Iraki murnar nasarar da ta samu a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci. Yana mai cewa, hakan wata babbar nasara ce ga hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da ayyukan ta'addanci. Kasar Sin tana fatan kasar Iraki za ta cimma nasara a kokarin da take na tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar kasar nan da nan.
A ranar Asabar din da ta gabata ce firaministan Iraki Haider al-Abadi ya ayyana nasarar sake kwato daukacin yankunan kasar da dakarun kasar suka yi daga hannun mayakan kungiyar IS. (Ibrahim)