A safiyar yau, babban manajan kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin Lu Dongfu ya sanar da wannan kuduri a nan birnin Beijing.
Lu Dongfu ya bayyana cewa, sakawa jirgin kasa mafi sauri na kasar Sin da suna "Fuxing" ya shaida hidimar jiragen kasa ya sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kyautata zaman rayuwar jama'a.
An ce, a ranar 26 ga wannan wata, jirgin kasa mai dauke da sabon suna "Fuxing" zai fara tafiya karo na farko a tsakanin tashar jiragen kasa ta Beijing da ta Shanghai, lambar jirgin kasan ita ce G123 da G124. (Zainab)