Liu Zhenmin ya bayyana cewa, Sin ta kara samar da gudummawa wajen gudanar da harkokin kasa da kasa a shekarar 2017, musamman kan tinkarar sauyin yanayi, da kawar da talauci, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, har an rubuta tunanin tabbatar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama da shawarar "ziri daya da hanya daya" da sauransu a cikin muradun MDD.
Haka zalika, Liu Zhenmin ya ce, za a tabbatar da burin kubutar da manoman yankunan karkara daga kangin talauci bisa ma'aunin kasar Sin na yanzu nan da shekarar 2020, wanda zai zama muhimmiyar gudummawar da kasar Sin ta samarwa dan Adam. (Zainab)