Shugaban Sin zai fidda sakon taya murnar sabuwar shekara ga kasa da kasa a yau Lahadi
Yau ranar 31 ga watan Disamba, shekarar 2017 da dare, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fidda sakon taya murnar sabuwar shekarar 2018 ga kasa da kasa, ta Gidan Rediyon CRI, da Gidan Rediyon CNR, da Gidan talabijin na CCTV, da Gidan talabijin na CGTN da kuma ta shafunan yanar gizo.
Haka kuma, Gidan Rediyon CRI zai watsa sakon shugaba Xi da harsunan waje guda 65 ga kasashen duniya da misalin karfe 11, agogon UTC. (Maryam)