Forfesa na jami'ar Kyorin ta kasar Japan Liu Di ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba kan kirkire-kirkire wajen kimiyya da fasaha a kasar Sin, wanda ya inganta darajar kamfanonin kasar Sin. Kana wannan ya canja fannoni daban daban na zamantakewar al'ummar kasar Sin da amfanawa jama'ar kasar.
Dan jarida na jaridar Pyramid daily ta kasar Masar Samy Elkamhawy, ya bayyana cewa, jawabin shugaba Xi Jinping ya sake tabbatar da burin kubutar da manoman kauyuka daga talauci bisa ma'aunin kasar Sin na yanzu nan da shekarar 2020, wannan ya shaida cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi bincike da nazari sosai kafin fitar da manufofinta. Ana gudanar da tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata, kuma an samu sakamako mai gamsarwa, musamman ma wajen yaki da talauci. (Zainab)