in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gabatar da gyare-gyaren da kasar ke fatan aiwatarwa a shekara 2018
2017-12-29 19:26:44 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada muhimmancin aiwatar da gyare-gyare a sabuwar shekarar ta 2018, a daidai lokacin da kasar ta Sin ta ke bikin cika shekaru 40 da kaddamar da shirin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaba kwamitin kolin sojan kasar, ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron murnar sabuwar shekara da babban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasan kasar ya shirya.

Shugaba Xi ya ce, a shekara ta 2018, ya kamata a kara zage damtse wajen aiwatar da sakamakon babban taron wakilan JKS na 19, da samun bunkasuwa cikin lumana, da ci gaba da raya tattalin arzikin kasa da zamantakewar al'umma yadda ya kamata.

Yayin da ya waiwayi baya kuwa, shugaba Xi ya ce, shekara ta 2017 dake shirin karewa, tana da muhimmanci ga ci gaban jam'iyya da ma kasar baki daya, ganin yadda a shekarar ce aka cimma nasarori da dama a dukkan fannonin tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin.

Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta bunkasa tsarin diflomasiyarta a dukkan sassa, sannan ta himmatu wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.

Shugaban kasar ta Sin ya ce, batun tafiyar da harkokin jam'iyya bisa doka abu da zai ci gaba, kana a shekarar ce aka kara daura damarar yaki da cin hanci da rashawa. Haka kuma a shekarar 2017 ce kasar Sin ta aiwatar da gyare-gyare a dukkan fannnoni, inda aka yi nasarar aiwatar da muhimman gyare-gyare guda 79, kana aka aiwatar da gyare-gyare 211 a manyan sassa baya ga wasu gyare-gyare 399 da ake fatan aiwatarwa a sassa daban-daban.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China