in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya hori dalibai Sinawa a jami'ar Moscow da su jajurce don cimma burukansu
2017-12-31 15:24:48 cri
A jiya Asabar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci dalibai Sinawa dake karatu a jami'ar Lomonosov dake Moscow da su sadaukar da kansu, da nuna kishin kasarsu, kana su yi aiki tukuru wajen cimma burukan da suka sanya a gaba.

Xi, kuma babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, CPC, kana shugaban kwamitin tsakiya na rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan kiran ne a cikin amsar wasikar da ya aikewa daliban da suka aikowa shugaba Xi don bayyana yadda suka fahimci tasirin da babban taron jam'iyyar CPC karo 19 yake da shi ga ci gaban kasar.

Ya ce, yana fatan daliban za su sadaukar da kansu domin neman ilmin da zai amfanawa kasarsu ta haihuwa da kuma al'ummar kasar baki daya, kuma su yi amfani da lokacin kuruciyarsu wajen cimma burin mafarki da suka dade suna yi a zukatansu.

Shugaba Xi ya kuma aike da sakon murnar sabuwar shekara ga dukkan dalibai Sinawa dake karatu a kasashen ketare. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China