in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaba Xi Jinping na kasar Sin don murnar sabuwar shekarar ta 2018
2017-12-31 19:00:07 cri

A jajiberin sabuwar shekara ta 2018, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabi don murnar sabuwar shekara, ta gidajen rediyoyin kasar Sin CRI, da gidan rediyon jama'ar kasar Sin CNR, da gidan telebijin na CCTV, da gidan telebijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN da ma yanar gizo ta Internet.

Yanzu ga cikakken jawabin da shugaba Xi ya gabatar:

Abokan aiki da na arziki, maza da mata:

Barka yamma! lokaci na wucewa cikin sauri. Yanzu muna maraba da sabuwar shekara ta 2018. A nan ne nake yi wa 'yan kabilu daban daban na kasarmu, da 'yan uwanmu na yankunan musamman na Hong Kong da Macao, da lardin Taiwan da ma Sinawa 'yan kaka gida murnar sabuwar shekara. Kana kuma ina fatan abokanmu da ke sassa daban daban na duniya za su cika burinsu a shekara mai zuwa.

Allah yana yabawa wadanda suke kokarin yin aiki, sannan kome na samun sauye-sauye a kullum. A shekarar 2017, mun gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 19, wanda ya fara sabon aikinmu na raya kasarmu ta gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni. Jimillar GDP da kasarmu ta samu ta wuce kudin Sin yuan biliyan dubu 80. Karin mutane fiye da miliyan 13 sun samu aikin yi a duk fadin kasar. Sannan mutane fiye da miliyan 900 suna cin gajiyar inshorar tsoffi. Haka kuma, mutane kimanin biliyan 1.35 suna cin gajiyar inshorar lafiya, yayin da wasu fiye da miliyan 10 suka fitar da kansu daga kangin talauci a yankunan karkara. A cikin wata tsohuwar waka, an ce, "Idan an samar da gidaje masu tarin yawa, wadanda suke fama da talauci za su yi farin ciki sosai." Yanzu, masu fama da talauci kimanin miliyan 3 da dubu 400 sun fara sabon zaman rayuwarsu a sabbin wurare, inda suka samu sabbin gidaje, sun fita daga talauci. Sa'an nan kuma, an kammala yin kwaskwarima kan gidaje marasa inganci miliyan 6 kafin lokacin da aka tsai da. Kasar Sin ta gaggauta raya ayyukan jin dadin jama'a iri daban daban, yayin da yanayin muhalli yake ta samun kyautatuwa. Jama'ar Sin sun kara jin dadin zamansu cikin tsaro. A hakika dai, Kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni.

1  2  3  4  5  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China