in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a Iran ya karu zuwa 141
2017-11-13 13:34:04 cri
Gidan talabijin na IRIB TV na Iran ya ce mutane a kalla 141 ne suka mutu, yayin da kusan dubu suka jikkata, sanadiyyar wata girgizar kasa mai karfin maki 7.2 da ta auku jiya Lahadi, a yankin kan iyakar Iran da Iraki.

Girgizar ta auku ne kilomita 103 daga kudu maso gabashin birnin Sulaymaniyah ta Iraki, kuma an ji amonta a larduna da dama na Iran dake iyaka da Iraki.

Sama da kauyuka 20 na lardin Kermanash na Iran ne suka lalace, inda hanyoyin wutar lantarki da na ruwa suka katse.

Sama da kungiyoyin bada agaji 30 na Iran ne aka tura yankin da girgizar ta auku, inda jirage masu saukar ungulu ke kai taimako ga mutanen da iftala'in ya aukawa.

Jami'ai sun ce girgizar ta yi sanadin mutuwar mutane 6 tare da jikkata wasu sama da 150 a lardin Sulaimaniyah na Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu na kasar Iran, ya ruwaito ma'aikatar lafiya ta Turkiyya na mika bukatar bada taimako ga yankin arewacin Iraki,

Haka zalika sauran hukumomin bada agaji, inda hukumar aikin ceto ta duniya IRC ta ce, ayarin jami'inta masu kai agaji na bibiyar al'amarin inda suke zaune cikin shirin kai dauki. (Fa'iza Mustaphha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China