in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta gudanar da kididdigar tattalin arziki a karo na hudu
2017-12-10 12:25:54 cri
Majalisar koli kan sha'anin mulki ta kasar Sin ta ba da sanarwa cewa, a shekarar 2018 mai kamawa za ta gudanar da wata kididdiga don sanin muhimman al'amurra game da tattalin arzikin kasar.

A bayanan da majalisar kolin ta kasar Sin ta fitar ta nuna cewa, wannan kidaya za ta shafi dukkan manyan matakan kasuwanci da kuma matakai na biyu, kana wannan kidaya za ta taimakawa kasar wajen shirya wani tsari da ya shafi harkokin tattalin arziki.

Sanarwar ta ce, wannan kididdiga za ta tattaro bayanai ciki har da na wadanda suka mallaki masana'antu, da yanayin karfin jarin masana'antun, da adadin kayayyakin da masana'antun ke samarwa, da karfin makamashin da suke bukata, da fasahar zamani da suke amfani da ita, da yadda suke aiwatar da ciniki ta hanyar yanar gizo, da kuma yanayin bincike da irin ci gaba da ake samu a harkokin cinikayyar.

Haka zalika sanarwar ta bukaci majalisun mulki na kananan hukumomi da su magance duk wasu matsaloli da suka jibinci gudanar da kidayar, ciki har da kaucewa amfani da alkaluman bogi, da jirkita sakamakon alkaluman da aka samu, da kuma yin shisshigi kan harkokin gudanar da kidayar.

A lokacin gudanar da aikin, majalisar mulkin kasar ta Sin za ta kafa wani tsarin da zai karfafa yadda za'a gudanar da aikin kidayar.

Majalisar tsakiya da majalisun kananan yankuna ne za su dauki nauyin kudaden gudanar da aikin kidayar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China