in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya ya sha alwashin yaki da ta'addanci
2017-12-01 09:19:56 cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya lashi takobin yin galaba a yaki da ta'addanci, inda ya bukaci al'ummar kasar da su hada karfi da karfe don dakile 'yan ta'adda dake hallaka rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kasar.

Kenyatta ya ce 'yan ta'adda suna yunkurin raba kan jama'a, da sanya kiyayya a tsakanin jama'ar kasar Kenyan amma basu samu nasara ba.

Shugaban ya yabawa kokarin da dakarun tsaron kasar KDF ke yi, wajen sadaukar da kansu domin tabbatar da tsaron kasar Kenya, musamman ta bangaren yaki da ta'addanci.

Da yake jawabi a lokacin da ya jagoranci bude faretin sojojin kasar a kwalejin horas da sojojin ta Lanet dake yankin Nakuru, Kenyatta ya ce, zasu samu galaba a fagen yaki da ta'addanci a kasar.

Shugaban kasar ya bayyana cewa cigaban Kenya ya dogara ne kan muhimman batutuwa da suka hada da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da shugabanci na gari, da cigaban tattalin arzikin kasa, su ne zasu tabbatar da daga darajar al'ummar kasar da inganta yanayin zamantakewa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China