in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin shugaba Xi ya gana da Kenyatta
2017-11-30 09:56:23 cri

Wang Jiarui, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a jiya Laraba, bayan ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Kenya a ranar Talata a Nairobi.

Wang, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kasance mafi daraja a tarihi, yayin da hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen ke ci gaba da samun tagomashi, kana mu'amala tsakanin al'ummomin kasashen biyu na kara dagawa zuwa matsayin koli.

Wang ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da kasar Kenya wajen aiwatar da yarjejeniyar Johannesburg wanda aka cimma matsaya a lokacin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, da zurfafa hadin gwiwa game da shawarar "ziri daya da hanya daya", da kuma ci gaba da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasashen zuwa babban mataki.

A nasa bangaren, Kenyatta ya godewa kasar Sin sakamakon irin goyon bayan da take baiwa kasarsa da kuma taimakon da take bayarwa wajen gina ci gaban al'ummar kasar Kenya da ci gaban tattalin arzikin kasar a shekaru masu yawa, ya kara da cewa kasar Kenya a shirye take ta yi aiki da kasar Sin wajen daga martabar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwa wajen gina ababen more rayuwa, da rage radadin talauci, da inganta yanayin zaman rayuwar jama'ar kasar, da kuma karfafa yin musaya tsakanin harkokin gudanar da sha'anin mulki na kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China