in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta shirya taron baje kolin hajojin masana'antu na Sin da Afirka
2017-12-09 12:11:14 cri

A mako mai zuwa ne za a kaddamar da baje kolin hajojin masana'antu na Sin da Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya, a wani mataki na gabatar da tarin damammaki da Kenya ke da su a fannin zuba jari.

Shugaban ofishin dake lura da harkokin cinikayya a ofishin jakadancin Sin dake kasar ta Kenya Guo Ce ne ya tabbatarwa manema labarai hakan, yana mai cewa baje kolin zai gudana ne tsakanin ranekun 13 ga watan Disamba zuwa 16 ga watan na Disamba.

Guo ya kara da cewa, ofishin bunkasa kasuwanci na kasa da kasa na Sin, da hadin gwiwar asusun samar da ci gaba na Afirka, da hukumar dake lura da hada hadar zuba jari ta Kenya ko KenInvest a takaice, su ne za su jagoranci shirya taron.

Mr. Guo ya ce kasar Kenya ta tabbatarwa duniya ikon ta na samun bunkasuwar tattalin arziki, wanda hakan zai dada jawo mata jari daga kasashen ketare.

Kaza lika jami'in ya bayyana kyakkyawan fatan sa, game da kafuwar gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta, bayan da ya lashe zabe a karo na biyu. Ya ce shekaru 5 masu zuwa na mulkin shugaban, za su haifarwa Kenya ci gaban tattalin arziki, da kara inganta yanayin zuba jari, da kyautata ayyukan hukuma, matakin da ko shakka babu zai jawo hankalin Sinawa masu sha'awar zuba jari.

A nasa tsokacin, babban manajan KenInvest Moses Ikiara, kira ya yi ga 'yan kasuwar kasar Kenya, da su yi amfani da wannan dama wajen tallata hajojin su yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China