A ranar Litinin MDD ta sanar da cewa, Jeffrey Feltman, jami'in dake kula da harkokin siyasa na ofishin sakatare janar na MDD, zai kai ziyarar aiki a Koriya ta arewa tsakanin ranakun Talata zuwa Juma'a.
Geng ya shedawa 'yan jaridu cewa, a ziyarar da Feltman ya kawo kwanan baya a kasar Sin, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, kuma manyan jami'an biyu sun yi musayar ra'ayoyi game da wasu muhimman batutuwa da suka shafi MDDr. (Ahmad Fagam)