Mr. Lu Kang na wannan tsokaci ne gabanin ziyarar aiki da ministan harkokin wajen Koriya ta kudu Kang Kyung-wha zai gudanar a nan kasar Sin, tsakanin ranekun 21 zuwa 23 na watan Nuwambar nan da muke ciki, inda ake fatan mahukuntan kasashen biyu za su tattauna da juna game da al'amura dake janyo hankulansu.
Kakakin ya kuma yi fatan ganin Koriya ta kudu ta kara azama, wajen bunkasa dangantakar kasashen biyu cikin lumana da wanzuwar ci gaba mai dorewa, domin a kai ga fadada hadin gwiwa, wanda zai amfani al'ummun kasashen biyu, tare da wanzar da zaman lafiya da daidaito, da ma ci gaba, da wadata a dukkanin yankin da suke. (Saminu Hassan)