Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada bukatar ginawa, kula da kuma amfani da hanyoyin dake yankunan karkara a yakin da mahukunta ke yi na kawar da talauci.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan gabanin taron sufuri na kasa da ya gudana a yau Litinin, ya ce ya kamata a kara zage dantse wajen gina hanyoyi a yankunan karkarar kasar, sannan a kula da su don tabbatar da inganta rayuwar manoma tare da zamanantar da aikin gona a kasar.
Xi ya ce, matakan da gwamnati ta dauka na inganta hanyoyin yankuna karkara sun haifar da gagarumin sakamako a 'yan shekarun nan, da samar da alheri ga karin jama'a da albarka ga yankuna masu fama da talauci da yadda JKS ta kara samun goyon bayan daga jama'a.
A cikin shekaru biyar din da suka gabata, kasar Sin ta gina ko gyara hanyoyin da suka kai kilomita miliyan 1.28, adadin da ya kai kaso 99.24 cikin 100 na hanyoyin birane da kaso 98.34 na kauyukan da aka hade su da hanyouyin kwalta ko siminti. (Ibrahim)